Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wata kafar yada labarai ta Isra'ila ta bayyana cewa, sakamakon hare-haren na Yemen, tashar jiragen ruwa ta Eilat ta tsaya cik gaba daya kuma an manta da ita.
Rashin kulawa da bayar da muhimmanci ga tashar jiragen ruwa na Ummar-Rashash (Eilat) ya shafe fiye da shekaru biyu yana gudana sakamakon hare-haren Yemen a lokacin yakin Gaza da kuma rashin wata cibiyar gwamnati da ta dauki nauyi.
Jaridar Yedioth Ahronoth: "Ayyukan tashar jiragen ruwa na Eilat ya ragu da fiye da 85% saboda barazanar Ansarullah da suka wanzu a cikin Bahar Maliya, wanda ya haifar da asarar fiye da dala biliyan 30".
Har ila yau, jiragen yaƙi marasa matuka na Iran sun kai hari a tashar jiragen ruwa a lokacin yakin kwanaki 12; tashar jiragen ruwa da aka sanya za ta kasance wani ɓangare na aikin layin ruwa na Bangorion.
Your Comment